sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane.
Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.
“Na daddatse al’ummai; an kuma rurrushe kagararsu. Na bar titunansu ba kowa, ba mai ratsawa a ciki. An ragargaza biranensu; ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.
Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”