Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba.
Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
“Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa.