Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 21:43 - Sabon Rai Don Kowa 2020

43 “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

43 “Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 21:43
13 Iomraidhean Croise  

za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”


A buɗe ƙofofi saboda al’umma mai adalci ta shiga, al’ummar da mai aminci.


Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.


Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.


Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”


Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?


Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”


Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”


Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.


In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.


Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan