Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:13 - Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

13 Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:13
29 Iomraidhean Croise  

Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima.


A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”


A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,


don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,


Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.”


Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.


Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.


Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.


Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,


Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.


Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,


Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.”


Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima.


Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”


Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.


Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.”


Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su.


Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.


Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”


Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.


Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.


Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.


Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.


Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.


Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan