Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:8 - Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

8 In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:8
22 Iomraidhean Croise  

Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”


Masu zunubi a Sihiyona sun firgita; rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa, “Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci? Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”


Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?


Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”


“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.


“Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”


Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’


Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.


shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.


Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.


Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan