Mattiyu 18:31 - Sabon Rai Don Kowa 202031 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki31 Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana. Faic an caibideil |