Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:25 - Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

25 Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:25
8 Iomraidhean Croise  

Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan.


To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”


Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,


Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”


Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.


Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”


Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan