11 Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.
11 Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa.
Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”
Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”
Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”
Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”
Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.