Mattiyu 13:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’ Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki15 Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’ Faic an caibideil |