Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe.
“Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”
Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.
“Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
“Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan ’ya’yan Set.
Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”
Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”