Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:10 - Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

10 Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa, “ ‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:10
10 Iomraidhean Croise  

Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.


“Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.


“Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo.


Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma.


su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”


Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”


An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa, “Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka,”


“Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,


Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan