Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.
“An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga.
Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”