Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.
“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar, ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci, birni ya yi gāba da birni, mulki ya yi gāba da mulki.
’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.
Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.”
Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”