Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.” Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.”
Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin Ubangiji yana raye, ko gashin kansa ɗaya ba zai fāɗi a ƙasa ba, gama abin da ya yi yau, Allah ne yana tare da shi.” Ta haka mutane suka ceci Yonatan daga mutuwa.