Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:12 - Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:12
20 Iomraidhean Croise  

Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.


A shekara ta talatin da bakwai ta bautar Yehohiyacin sarkin Yahuda, a shekaran da Ewil-Merodak ya ci sarautan Babilon, sai ya saki Yehohiyacin daga jaru, ya sake shi a rana ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu.


Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,


Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah.


Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu.


Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa. Serahiya, Irmiya, Ezra,


“Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.


Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?


Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”


waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,


A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji.


Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu,


“Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce,


“ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan ɗauke ka, bawana Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel,’ in ji Ubangiji, ‘in kuma maishe ka kamar zoben hatimi, gama na zaɓe ka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”


Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.


Zerubbabel ya haifi Abiyud, Abiyud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor,


Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.


ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan