Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.
“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’ ”
“A wannan rana zan maido da tentin Dawuda da ya fāɗi. Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage, in kuma maido da kufansa in gina shi kamar yadda yake a dā,
A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu.
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”
Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.
Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya.
Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.
Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi.