Amma sa’ad da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon da kuma Geshem mutumin Arab suka ji game da wannan, sai suka yi mana ba’a suka kuma yi mana dariya. Suka ce, “Me kuke tsammani kuke yi? Kuna so ku yi wa sarki tawaye ne?”
Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.
Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”