Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.
Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
“ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu.
A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.