Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki za ku kuma aske kawunanku. Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.