Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 3:59 - Sabon Rai Don Kowa 2020

59 Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

59 Ka ga laifin da aka yi mini, Sai ka shara'anta da'awata, ya Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 3:59
16 Iomraidhean Croise  

Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.


Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”


Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu


Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.


Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.


Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.


Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane.


Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.


Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina.


ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?


Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.


Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan