saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa.
Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ”
“Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.
Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.
“Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi.