Ka duba daga sama ka gani daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka. Ina kishinka da kuma ikonka? Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.
“Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?