Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.
“Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa.
Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.
“Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”
Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.