47 Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
47 Tsoro, da wushefe, Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.
Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?
“Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.
Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani, ’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.
Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.