Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.
In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.
Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta; ba ka amince da abin da ke ba daidai ba. To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka? Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?
Idan mūsu ya tashi tsakanin mutum biyu har abin ya kai su kotu, alƙalai kuwa suka yanke hukunci a kan batun, suka kuɓutar da marar laifi sa’an nan suka hukunta mai laifi,