Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji.
“Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma.
Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, za a yanke su, a kawar a su. Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, ba zan ƙara ba ki azaba ba.