Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.
“Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’
Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.