Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ”
Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.
Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka.
Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.