Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’
Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji.