Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:4
38 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”


Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’


Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa.


Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.


Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.


Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.


Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa, yaƙi mai tsanani. Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba; ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.


Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su.


Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”


An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke. ’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka.


Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.


Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma.


Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke.


Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.”


Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta.


Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’


“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba.


“Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.


Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda.


ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.


Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.


Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.


“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka.


Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi.


Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ”


“Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata,


Saboda haka na husata da su domin sun yi kisankai a ƙasar kuma domin sun ƙazantar da ita da gumakansu.


“Sa’an nan ne fushina zai huce hasalata a kanki kuma ta lafa, in kuma wartsake. Kuma sa’ad da na zuba fushina a kansu, a sa’an nan ne za su san cewa Ni Ubangiji na yi magana a cikin fushin kishina a kansu.


Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.


“ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome, ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.


Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.


Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.


Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.


Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.


Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan Ubangiji ya rabu da kai? Ya zama maƙiyinka?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan