Makoki 2:22 - Sabon Rai Don Kowa 202022 “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki22 Ka gayyato mini tsoro Kamar yadda akan gayyato taro a ranar idi. A ranar fushin Ubangiji Ba wanda ya tsere, ko wanda ya tsira. 'Ya'yan da na yi renonsu, na goye su, Maƙiyina ya hallaka su. Faic an caibideil |
Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’