Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

20 Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:20
24 Iomraidhean Croise  

Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.


aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.


Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma?


Ya kai gari cike da hayaniya, Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna? Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba, ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.


Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’


Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’


Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe?


“Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa.


Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena.


Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu.


Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.


Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska.


Sa’an nan ya ce musu, “Ku ƙazantar da haikalin ku kuma cika filayen da kisassu. Ku tafi!” Saboda haka suka fita suka kuma fara kisa a duk birnin.


Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata.


Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan