Makoki 1:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki7 A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta. Faic an caibideil |