Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

16 “Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:16
23 Iomraidhean Croise  

Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.


Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka.


Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.


Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya. Na ga hawayen waɗanda ake zalunta kuma ba su da mai taimako; masu iko suna goyon bayan masu zalunci, ga shi ba su da mai taimako.


“Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.


Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.


“Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa.


“Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi makoki dominki? Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki?


Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki, zuciyata ta ɓaci ƙwarai.


Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe.


Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada. Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta, ba a kuma jin kukan shanu. Tsuntsaye sararin sama sun gudu namun jeji ma duk sun watse.


Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali.


Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.


Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”


Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.


Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.


Ko da sun yi renon ’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan