Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 4:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

6 Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 4:6
21 Iomraidhean Croise  

Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.


Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.


Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.


“Muddin ina raye,” in ji Sarki, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, “wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu, kamar Karmel kusa da teku.


“Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.


Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”


Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,


Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”


Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun. Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.


Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.


Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,


Kedesh, Edireyi, En Hazor,


daga kabilar Naftali kuma aka ba su, Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan.


a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.


A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.


Ya aika manzanni ko’ina a Manasse, yana kiransu su kintsa, haka ma Asher, Zebulun da Naftali, ta haka su ma suka haura su sadu da su.


Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.” Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.”


“Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.


Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan