Mahukunta 17:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Sa’ad da ya mayar da azurfa dubu ɗaya da ɗari ɗaya na shekel wa mahaifiyarsa, sai ta ce, “Na ba da azurfata ga Ubangiji don ɗana yă sassaƙa sura yă kuma yi zubin gunki. Zan mayar maka.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki3 Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la'anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.” Faic an caibideil |
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;