Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 3:5 - Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

5 Za a cike kowane kwari, Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su. Za a miƙe karkatattun wurare, Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 3:5
11 Iomraidhean Croise  

Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau.


Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.


Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.


Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi, a kuma gyara manyan hanyoyina.


Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ”


Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan