Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.
Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.