Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 13:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi ’ya’ya ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

6 Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 13:6
14 Iomraidhean Croise  

Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji?


“ ‘Zan ƙwace girbinsu, in ji Ubangiji. Ba a za sami inabi a kuringa ba. Ba za a sami ’ya’ya a itacen ɓaure ba, ganyayensu kuwa za su bushe. Abin da na ba su za a ƙwace.’ ”


Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”


An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”


Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.


Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,


Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.


“Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan