Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 8:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

4 Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 8:4
11 Iomraidhean Croise  

Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin.


Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.


“Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.


Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan.


Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.


Ubangiji ya ce wa Musa,


Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”


Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan