Ƙidaya 6:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da 'ya'yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun 'ya'yan inabi. Faic an caibideil |