ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’ ”
Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima.
Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.