Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 27:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 “Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

3 “Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da 'ya'ya maza.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 27:3
16 Iomraidhean Croise  

Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.


Ni, Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata waɗannan abubuwa a kan dukan muguwar jama’an nan da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su sadu da ƙarshensu a wannan hamada; a nan za su mutu.”


Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron.


Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora.


(Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)


Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce,


Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”


Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”


Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”


Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.


domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.


Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan