Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 24:9 - Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Kamar zaki sun laɓe sun kwanta, kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su? “Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

9 Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 24:9
21 Iomraidhean Croise  

Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.”


Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”


Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?


Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki.


Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu.


Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!”


Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?


Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.


Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.


In kun kasa kunne sosai ga abin da yake faɗi, kuka kuma yi abin da na faɗa, zan zama magabci ga abokan gābanku, zan kuma yi hamayya da abokan hamayyanku.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.


Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai, a cikin mutane masu yawa, kamar zaki a cikin sauran namun jeji, kamar ɗan zaki cikin garken tumaki, wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu, ba kuwa wanda zai cece su.


Amma Allah ya ce wa Bala’am, “Kada ka tafi tare da su. Kada ka la’anta mutanen nan, gama su masu albarka ne.”


Ka zo yanzu ka la’anta waɗannan mutane, domin sun fi ƙarfina. Wataƙila zan iya cin nasara a kansu, in kuma kore su daga ƙasar. Gama na sani duk waɗanda ka sa musu albarka, sun zama masu albarka ke nan, waɗanda kuma ka la’anta, sun la’antu ke nan.”


Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya; sun tā da kansu kamar zaki wanda ba ya hutawa sai ya cinye naman abin da ya kama ya kuma sha jinin abin da ya kama.”


Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.


“Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’


“Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’


Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.


Ubangiji Allahnku zai sa dukan waɗannan la’anoni a kan abokan gābanku waɗanda suke ƙinku, suke kuma tsananta muku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan