Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 2:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

3-9 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka 186,400 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 2:3
19 Iomraidhean Croise  

Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.


’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.


Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.


ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne),


Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.


“Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;


daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;


Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya.


Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.


Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.


Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.


da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.


Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,


Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan