Ƙidaya 10:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Ubangiji ya ce wa Musa, Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, Faic an caibideil |
Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.