Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.
Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.