Hosiya 7:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 A ranar bikin sarkinmu shugabanni sukan bugu da ruwan inabi, yă yi cuɗanya da masu ba’a. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki5 A ranar bikin sarki, Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi. Yakan yi cuɗanya da shakiyai. Faic an caibideil |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.