Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Hosiya 2:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 “Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 “Ka ce wa 'yan'uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa 'yar'uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Hosiya 2:1
17 Iomraidhean Croise  

tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,


“Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.


Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.


Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda bai yashe su ba, ko da yake ƙasarsu cike da take da laifi a gaban Mai Tsarki na Isra’ila.


Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.


Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.


Za ku zauna a ƙasar da na ba wa kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.


Mazaunina zai kasance da su; zan kuwa zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.


“Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta tă daina karuwancinta da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.


Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”


Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”


Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba.


Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.


Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan