Hosiya 10:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki8 Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!” Faic an caibideil |
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.